Yadda Akayi Jana’izar Mutane 50 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar Zamfara

0 80

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa a yau ne za’a yi jana’izar wasu mutane da ‘yan bindiga suka hallaka, bayan wani mummunan hari da suka kai a wasu kauyuka 4 wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane.

Da maraicen ranar Laraba ne wasu shaidun gani da ido suka bayyanawa manema labarai cewa, sun kirga mutum 51 da aka kashe daga kauyuka 4 daga gundumar Magami ta karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.

Wannan mumunan lamarin dai ya afku ne kwana daya bayan da mutanen da suka rasa rayukansu suka yi yunkurin kai dauki ga mutanen garin ‘Yar Doka, wadanda wasu bayanai ke cewa sun koma gida daga gudun hijira ne, kwatsam kuma ‘yan bindigan suka dirar musu da wannan kazamin hari.

Majiyoyi daga kauyukan da lamarin ya shafa sun ce ya zuwa daren jiya, mutane na cigaba da tserewa daga kauyukan yankin zuwa gudun hijira a Magami mai nisan kimanin kilomita 18.

Shaidu sun bayyana cewa, mutanen da ‘yan bindigan suka kashe sun hada da akalla 20 daga kauyen Ruwan Dawa, sai wasu goma na Kangon Fari Mana, shida daga Madaba, wasu shida daga Arzikin, a yayin da kauyukan Mai Kogo da Mai Aya-aya da Mai Rairai, kowanne mutum biyu, sai Gidan Maza da Kunkelai mutum dai-daya kowannensu.

Wani shaida daga Kangon Fari Mana ya ce ‘yan fashin sun shafe kimanin sa’o’i bakwai suna cin karen su ba babbaka tare da harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Mutanen kauyen ‘Yar Doka da suka nemi dauki daga makwabtansu, sun koma gida ne kwana daya kafin wannan kazamin harin, don ganin ko akwai halin noma gonakinsu kamar yadda bayanai suka bayyana.

A cewar mazaunan yankin ‘yan bindigar sun dauki alkawarin cewa ba’za a yi noma ba a fadin gundumar Magami, kuma sun yi imanin cewa, wannan kuduri ne ya sanya su sake afka wa kauyen na ‘Yar Doka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: