Yadda Cutar Diphteria Ta Yi Barna A Jihohin Kano, Katsina da Filato

0 76

Yadda cutar diphteria ta yi ɓarna a jihohin Kano, Katsina da Filato

Cutar diphtheria na ci gaba da yaɗuwa a wasu sassan jihohin Filato, Katsina da Kano, inda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama yayin da ake fargabar ɗaruruwan mutane sun kamu da ita.

A Jihar Filato, alƙaluma sun nuna mutane 23 sun mutu sakamakon cutar a ƙananan hukumomin Jos North, yayin da ake zargin wasu 143 sun kamu.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Nicholas Baamlong, ya bayyana hakan a ranar Talata a wata hira da manema labarai a Jos, babban birnin jihar.

Ya ce mafi yawan mace-macen sun faru ne cikin makonni uku da suka gabata, yayin da gwamnati ke ƙara ƙaimi wajen daƙile yaɗuwar cutar.

Kwamishinan ya ce a halin yanzu an killace marasa lafiya tara da ke karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) da kuma Asibitin Ƙwararru da ke Filato.

Ya bayyana ƙarancin maganin diphtheria antitoxin da kuma jinkirin kai marasa lafiya asibiti a matsayin manyan ƙalubalen da ake fuskanta wajen yaƙi da cutar.

“Babban ƙalubalen shi ne samun antitoxin[maganin kashe ƙwayoyin cutar], sannan yawancin marasa lafiya suna zuwa asibiti ne bayan cutar ta yi tsanani,” in ji shi.

A cewarsa, cutar na yaɗuwa ta hanyar kusanci da mai ɗauke da ita, musamman ta tari da atishawa, yana mai kira ga jama’a da su ɗauki matakan kariya tare da gaggauta zuwa asibiti da zarar an fara ganin alamominta.

Ya kuma bayyana cewa jihar na fuskantar matsala wajen tabbatar da wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun kamu, saboda rashin wasu kwantena na musamman da ake amfani da su wajen tattara samfuran cutar da kai su dakunan gwaje-gwaje.

Baamlong ya ce an sanar da Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) game da lamarin, kuma jihar na fatan samun tallafi, musamman maganin kashe ƙwayoyin cutar da kuma robobin tattara samfura.

Ya ce gwamnati ta kuma ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a a al’ummomin da abin ya shafa, tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.

A nasa ɓangaren, Jami’in Sa-Ido da Sanar da Cututtuka (DSNO) na Ƙaramar Hukumar Jos North, Baks Bulus, ya ce ƙaramar hukumar ta samu mutane 117 da ake zargin sun kamu da cutar, inda 15 daga cikinsu suka mutu.

Bulus ya ce mutanen da suka yi mu’amala ta kusa da waɗanda suka kamu da cutar na cikin haɗarin kamuwa, musamman waɗanda suka yi amfani da kayan abinci, tawul da sauran kayayyakin gida iri ɗaya.

Ya ce yaran da aka yi wa cikakkiyar rigakafin cutar kan fuskanci alamomi masu sauƙi idan sun kamu, yayin da waɗanda ba a yi wa rigakafi ba ko kuma ba su kammala allurar da ake buƙata ba ke cikin haɗarin kamuwa da cuta mai tsanani da mutuwa.

Cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 30 a Katsina
A Katsina kuwa, gwamnatin jihar ta ce cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 30 daga cikin 34 da ke jihar.

Kwamishinan Lafiya, Alhaji Musa Adamu, ya bayyana hakan a wata hira da Aminiya a ranar Talata.

Sai dai akwai saɓani tsakanin gwamnatin jihar da Asibitin Koyarwa na Jamiar Taryya da ke Katsina (FTHKT) kan yawan mutanen da cutar ta kama da kuma waɗanda ta kashe.

Gwamnatin jihar ta ce an tabbatar da mutane 31 da suka kamu tun bayan sake ƙaruwar alƙaluman cutar kimanin makonni uku da suka gabata.

Sai dai jami’an FTHKT sun ce kusan mutane 150 da aka tabbatar sun kamu da cutar ne aka kwantar a asibitin cikin wannan lokaci, inda 29 suka mutu.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta ƙara ƙoƙarin daƙile cutar tare da kafa wasu cibiyoyin killace marasa lafiya guda uku a Daura, Funtua da Katsina.

Ya ce gwamnatin jihar, tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ci gaba da samar da alluran rigakafi, kayan aikin asibiti da sauran kayayyakin da ake buƙata wajen kariya da magance cutar.

A cewar Adamu, an samu mutane 1,837 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin jihar a bana, yayin da 719 suka je asibitoci da alamomin da suka yi daidai da cutar.

Ya bayyana diphtheria a matsayin cuta da ke ƙaruwa a wasu lokuta kuma ana iya kare kai daga gare ta ta hanyar rigakafi, yana kira ga iyaye da masu kula da yara su rungumi tsarin “gargadi da wuri, ɗaukar mataki da wuri” ta hanyar kai yaran da ake zargin sun kamu asibiti cikin gaggawa.

A nata ɓangaren, Mukaddashin Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Katsina, Dokta Shaima’u Kabir Abba, ta ce mutane 15 ne kawai aka tabbatar sun kamu da cutar a FTHKT, tana mai cewa adadin mace-macen da aka samu a jihar ya kai kashi 5.6 cikin 100.

Sai dai Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Lafiya na FTHKT, Dokta Abdulfatah Muhammad Lawal, ya ce kusan mutane 150 da aka tabbatar sun kamu da cutar aka kwantar a asibitin cikin wannan barkewar, inda 29 suka mutu.

Shugaban sashen kula da yara na asibitin, Dr Abdulrazak Alege, ya tabbatar da adadin, yana mai cewa mutane 29 sun mutu cikin kusan 150 da aka kwantar a cikin makonni uku.

Kano ta samu allurai 650,000

A Jihar Kano kuma, gwamnatin tarayya ta samar da alluran rigakafin diphtheria 650,000, amma gwamnatin jihar ta ce tana buƙatar aƙalla allurai miliyan tara domin daƙile cutar a ƙananan hukumomi 44.

Daraktan Hukumar Yaƙi da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ya tabbatar da isowar alluran a ranar Talata, yana mai cewa za a yi amfani da su wajen yi wa yara da tsofaffi rigakafi.

Ya ce adadin alluran da aka kawo bai wadatar ba, domin jihar na buƙatar miliyan tara.

Abbas ya kuma gana da dukkan hakiman gundumomin jihar a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, inda ya yi musu bayani kan halin da ake ciki tare da neman su taimaka wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa jama’a su je a yi musu rigakafi.

Ya ce yawancin mace-macen da aka samu sun shafi yaran da ba a yi wa rigakafin cutar ba da kuma waɗanda aka jinkirta kai su asibiti.

Daraktan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara neman waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a al’ummomin Rano, tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya, jami’an sa-ido da ma’aikatan lafiya.

Ya ce an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa tsarin sa-ido, inganta rahoton yau da kullum da kuma wayar da kan gidaje kan rigakafi.

Sai dai lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake takaddama kan ainihin adadin mace-macen cutar a jihar.

A makon da ya gabata, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Rano, Ibrahim Malami, ya yi zargin cewa sama da yara 50 ne suka mutu a yankin.

Sai dai KNCDC ta yi watsi da iƙirarin, tana mai cewa ba a tabbatar da shi ba kuma yana iya ɓatar da jama’a.

Abbas ya ce mutane biyu ne kawai suka mutu sakamakon cutar a Rano a shekarar 2026, yayin da jimillar waɗanda suka mutu a faɗin jihar tun bayan gano cutar a watan Yulin 2023 ta kai 29.

Gwamnatin jihar ta kuma ƙaddamar da wani kwamiti na musamman da zai jagoranci yaƙi da barkewar cutar, wanda ya ƙunshi jami’an ma’aikatar lafiya, KNCDC, Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko, Hukumar Kula da Asibitoci da kuma majalisun masarautun jihar.

Sama da mutum 10,000 sun kamu a bana — NCDC
A matakin ƙasa kuwa, Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an tabbatar da sama da mutane 10,000 da suka kamu da diphtheria a Najeriya a bana.

Darakta-Janar na hukumar, Dr Jide Idris, ya ce duk da yawan mutanen da cutar ta kama, adadin waɗanda ke mutuwa daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya ragu sosai idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Ya ce ƙarancin yawan yaran da ke samun cikakkiyar rigakafi na daga cikin manyan abubuwan da ke taimaka wa cutar yaɗuwa, musamman tsakanin yaran da ba a yi wa rigakafi ba ko kuma ba su kammala allurar da ake buƙata ba.

Ya kuma bayyana rashin tsaro, wuraren da ke da wahalar isa, gudun hijira da yawan zirga-zirgar jama’a a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga ƙoƙarin kai rigakafi ga duk yaran da suke buƙata.

Idris ya jaddada cewa diphtheria cuta ce da za a iya kare kai daga gare ta ta hanyar rigakafi, yana kira ga iyaye da masu kula da yara su tabbatar sun kammala dukkan alluran da ake buƙata.

Ya ce ana samun allurar rigakafin cutar kyauta a cibiyoyin lafiya ta hanyar shirin rigakafin yau da kullum da kuma kamfen na musamman.

Haka kuma ya buƙaci ma’aikatan lafiya su kasance cikin shiri wajen gane alamomin cutar, gaggauta sanar da hukumomi idan an samu wanda ake zargi da ita, tare da tabbatar da an ba marasa lafiya kulawar da ta dace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.