Atiku ya shirya tallafa wa matatun mai na cikin gida da ɗanyen mai – Abdullahi
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce shirin Atiku Abubakar kan tallafin man fetur ba zai kasance tallafin farashin fetur kai tsaye ba, sai dai tallafa wa matatun mai na cikin gida wajen samun ɗanyen mai a farashi mai sauƙi.
Ya ce hakan zai rage kuɗin tace man fetur, wanda daga ƙarshe zai iya sa farashin fetur ya sauƙaƙa wa ’yan Najeriya.
Abdullahi ya bayyana cewa gwamnati za ta iya ware wani kaso na ɗanyen man Najeriya ga matatun cikin gida a farashin da aka kayyade, maimakon su saya da farashin kasuwar duniya.
Sai dai ya ce har yanzu jam’iyyar na aiki kan ƙididdigar yawan kuɗin da shirin zai ci a shekara, kuma za ta bayyana cikakkun bayanai yayin yakin neman zaɓe.