Zazzabin Lassa: Adadin Waɗanda Suka Mutu Ya Kai 252 – NCDC

0 65

Zazzabin Lassa: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 252 – NCDC

Hukumar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a Najeriya ya kai 252, yayin da adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya koma 1,035.

Sabbin mutane 14 da aka tabbatar sun kamu sun fito ne daga jihohin Ondo, Bauchi, Edo da Benue. Ya zuwa mako na 33, jihohi 23 da ƙananan hukumomi 117 sun samu rahoton cutar.

NCDC ta ce adadin mace-macen ya kai kashi 24.4 cikin 100, lamarin da ya fi na shekarar 2025, inda ya kasance kashi 18.6.

Leave A Reply

Your email address will not be published.