Yan bindiga sun kai hari wata kasuwa inda suka kashe akalla mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama a jihar Filato

0 50

Yan bindiga sun kai hari wata kasuwa inda suka kashe akalla mutane  bakwai tare da jikkata wasu da dama a Jihar Filato.

Maharan sun yi wa Kasuwar Pinau dirar mikiya ne da yamma inda suka bude wa mutane wuta a yayin da ake tsaka da cin kasuwa.

Wani shugaban matasa a yankin, Shafi’i Sambo, ya ce ’yan bindigar na shiga kasuwar suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Manema Labarai sun gano cewa ’yan bindiga sun far wa kasuwar da ke unguwar Pinau da ke Karamar Hukumar Wase ta Jihar ne ranar Lahadi.

Sun kuma koka cewa masu hada baki da ’yan bindigar suna kawo cikas ga kokarin jami’an tsaro na magance matsalar.

Wata majiya a kauyen ta ce a kwana 10 da suka gabata ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a yankin kuma sun karbi miliyoyin kudade a matsayin kudin fansa.

An tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, domin samun karin bayani, sai dai jami’in dan sandan bai amsa kiran wayan ba ko rubutaccen sakon da aka tura mishi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: