‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da su a jihar Kebbi

0 114

Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da su a kauyen Kwarikwarasa da ke karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi.

A cewar rahoton, ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne da sanyin safiyar ranar Asabar domin kai harin.

Da yake jawabi a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa al’umma, gwamnan jihar, Nasiru Idris, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati ta dauki matakan dakile sake afkuwar lamarin. Ya kuma ce gwamnatin sa ta bai wa jami’an tsaro dukkan goyon baya da hadin kan da ya kamata wajen yakar miyagun laifuka a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: