Yan fashin daji akan babura kusan 300 sun kashe mutane 12 tare da raunata wasu 6 a jihar Katsina

0 131

Yan fashin daji, akan babura kusan 300, sun kashe mutane 12 tare da raunata wasu 6 a kauyen Duba na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, a ranar Asabar da dare.

An kuma kashe wasu mutane 2 tare da raunata wasu da dama a wasu hare-haren, kasancewar ‘yan fashin dajin sun cigaba da cin karensu babu babbaka a jihar dake fama da rashin tsaro.

An shafe awanni dayawa ana kaddamar da harin na kauyen Duba.

Kakakin yansanda na jihar, Gambo Isah, ya gayawa manema labarai cewa ‘yan fashin dajin sun mamaye kauyen dauke da muggan makamai.

Yace ‘yan fashin dajin sun tsere zuwa dajin dake kusa kafin zuwan yansandan ceto.

Wani mazaunin Batsari ya gayawa manema labarai cewa ‘yan fashin dajin sun isa kauyen da misalin karfe 11 na dare.

Yan fashin sun yashe shaguna da gidaje, tare da cinnawa wasu gine-gine wuta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: