‘Yan fashin daji sun kai sumame garin karamar hukumar Jibia inda suka kashe mutum 1 da raunata wasu guda 3

0 75

‘Yan fashin daji a jiya sun kai sumame garin Kukar Babangida a yankin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda suka kashe mutum guda tare da raunata wasu mutane 3.

Mazauna garin sun ce yan fashin sun iso garin da misalin karfe 11 na dare inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi, tare da bi gida-gida suna neman dabbobi da sauran abubuwan da zasu sace.

Bayan sun gama aika-aikar, ‘yan fashin dajin sun yi awon gaba da dabbobi 300 da babura tare da kayan sawa.

Mutane ukun da suka samu rauni, suna samun kulawa a asibitocin dake kusa.

Garin na Kukar Babangida, dake kan titin Katsina zuwa Jibia, ya zama mafakar ‘yan gudun hijira wadanda hare-hare ya shafa a kauyukan Jibia.

Tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ne ya sakewa garin suna, lokacin da tsaya a garin ya shuka bishiyar Kuka, bayan wata ziyarar aiki da ya kai Katsina a shekarun 1980.

Leave a Reply

%d bloggers like this: