Dan Maganar Dutse ya cika shekara biyar, ya godewa Sarkin Dutse

0 101

Alhaji Shu`aibu Ali `Yar gaba ya cika shekaru biyar samun sarautar Dan Maganar Dutse wadda Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Nuhu Muhammad Sanusi ya tabbatar masa. Ranar da ya cika shekara biyar cif itace ranar Alhamis 15 ga watan Yuli 2021.

Kamar yadda Mahangar arewa suka ruwaito, yace “Ina godiya ga Allah Subhanahu Wa ta’ala da ya kawo mu wannan rana da ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwa ta, Ina kira ga al’uma da su dukufa noman damina da na rani saboda ayi naganin matsalar kayan masarufi da yake faman tsada a wannan lokaci, Ina kuma kara kira ga al’umma da a koma ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala ta wajen rokonsa gafara akan kurakuren mu kamar yadda har kullum Mai martaba Sarkin Dutse Alh Dr Nuhu Muhammad Sanusi ya ke jan hankalin mutane a ko da yaushe.

“Ina kuma kira ga al’umma da su rinka kula da wadanda suke mu’amula da kuma za suyi mu’amular da su saboda matsalar tsaro da ake fama da ita, Ina addu’ar Allah ya sa ayi bukukuwan sallah lafiya ya kara kawomana zaman lafiya, kwanciyar hankali da karuwar arziki a wannan masarauta tamu ta Dutse da jihar Jigawa da ma kasa baki daya”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: