’Yan Nijeriya 5,000 dake gudun hijira a Kamaru sun fara komawa gida

0 126

Yan Nijeriyar da suka tsere zuwa Kamaru, dalilin ayyukan kungiyar BH, sun fara komawa gida a jiya Litinin, bisa radin kansu.

Kashin farko da ya kunshi ’yan gudun hijira 5,000, wadanda suka kwashe shekaru 6 a sansanin Minawao dake Kamaru ne suka kama hanyar komawa gida a jiya cikin motocin bas.

Da yake ganawa da ’yan gudun hijirar jim kadan kafin tashinsu daga Maroua, babban birnin yankin arewa mai nisa na Kamaru, ministan kula da yankunan kasar, Paul Atanga Nji ya ce, an dauki dukkan matakan da suka kamata na tabbatar da tafiyar ta gudana lami lafiya.

Sama da ’yan Nijeriya 57,000, galibinsu daga jihar Borno ne suka nemi mafaka a sansanin Minawao dake Mokolo na yankin arewa mai nisa na Kamaru

Leave a Reply

%d bloggers like this: