‘Yan sanda sun kwato ababen fashewa 8 da alburusai 8,000 a jihar Rivers

0 424

Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta bayyana cewa ta kwato ababen fashewa guda takwas (8) da kuma alburusai sama da 8,000, tare da kama mutum 33 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Olugbenga Adepoju, ne ya bayyana hakan yayin taron bayyana wadanda ake zargi a garin Port Harcourt ranar Alhamis.

Ya ce an samu wannan nasara ne cikin watanni bakwai da suka gabata, da haɗin gwiwar sojojin ƙasa, sama da ruwa, tare da jami’an DSS, NSCDC, da sauran hukumomin tsaro.

Daga cikin wadanda aka kama akwai ’yan kungiyar asiri bakwai, ciki har da wadanda ake zargi da kisan wani lauya, Bright Owhor, a unguwar D/Line ta birnin Port Harcourt.

Leave a Reply