Shahararren attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya kulla yarjejeniya da gwamnatin Habasha domin gina sabuwar masana’antar taki da aka kiyasta za ta lashe dala biliyan 2.5. Za a gina wannan katafariyar masana’anta a yankin Somali na gabashin Habasha, tare da Dangote yana da kashi 60 cikin 100 na hannun jari, yayin da gwamnatin Habasha ke da kashi 40 ta hannun Ethiopian Investment Holdings (EIH).
Ana sa ran za a kammala aikin cikin watanni 40, kuma za ta rika fitar da tan miliyan uku na taki a shekara. Masana’antar za ta samu iskar gas kai tsaye daga filayen Calub da Hilala. Gwamnatin Habasha ta ce wannan aiki zai taimaka wajen rage shigo da taki daga waje da kuma kara karfin tattalin arzikin cikin gida.
Firayim Minista Abiy Ahmed ya bayyana aikin a matsayin muhimmin ci gaba ga samar da wadataccen abinci da kuma kirkirar ayyukan yi. Dangote ya ce hadin gwiwar na nuni da burinsu na bunkasa masana’antu da cimma isasshen abinci a nahiyar Afrika.