Hukumar National Youth Service Corps (NYSC) ta fitar da jadawalin fara yin rijista na Batch B Stream II na shekarar 2025, inda ta bayyana ranakun da za a farayi ga masu shirin yin bautar ƙasa.
A cewar sanarwar da aka wallafa a shafinta na X da kuma shafin yanar gizo na hukumar, za a fara rajistar masu digiri daga Najeriya da ƙasashen waje daga ranar Litinin, 8 ga Satumba zuwa 13 ga Satumba, 2025.
Hakazalika, an tsara cewa binciken takardu na ‘yan ƙetare da za su shiga shirin za a gudanar da shi daga 14 zuwa 18 ga Satumba, 2025.
Sashen ICT na NYSC zai gudanar da ayyukansa na tsarin kwamfuta tsakanin 17 zuwa 20 ga Satumba, 2025.
A cewar NYSC, makarantun da ke fitar da ‘yan hidima za su fara bugawa tare da raba takardun tura wuri (call-up letters) daga ranar 21 zuwa 23 ga Satumba, 2025. A wannan lokaci, masu shirin hidimar ƙasa (PCMs) suma za su iya shiga shafin yanar gizo don buga nasu takardu.