Gwamnati ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a jihohi 14

0 1,304

Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta yi gargaɗi kan yiwuwar ambaliya a jihohi 14, inda ta ce akwai yiwuwar ruwan sama mai yawa daga 4 zuwa 8 ga Satumba, 2025, a wurare 43 a faɗin ƙasar.

Sanarwar, wadda aka fitar a ranar Alhamis, ta fito ne daga Cibiyar da take kula da harkokin ambaliya ta hukumar kula da muhalli ta Ƙasa, tare da sa hannun Daraktan Sashen Sarrafa Ambaliya da Lalacewar Gabar Teku, Usman Abdullahi Bokani.

Jihohin da aka fi hasashen za su fuskanci ambaliya sun haɗa da:
Ebonyi, Cross River, Kano, Zamfara, Taraba, Abia, Yobe, Plateau, Borno, Imo, Niger, Sokoto, Kaduna da Akwa Ibom.

Gwamnati ta ce matsalolin sauyin yanayi da rashin kyakkyawan tsarin magudanar ruwa na daga cikin dalilan da ke haddasa ambaliya.

A wani mataki na tallafi, Gwamnatin Sin ta bai wa Najeriya $1 miliyan don rage radadin ambaliya a jihohin Arewa.

Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ya tabbatar da cewa an tanadi tsarin da zai tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon tallafin.

Leave a Reply