Yan Sandan Nigeria Na Shirye Shiryen Magance Matsalolin Tsaro Yayin Bukukuwan Easter

0 76

Babban safeton yan sanda na kasa Usman Alkali Baba ya umarci kwamishinonin yan sanda da su aike da jami’an su zuwa domin yin aiki a wuraran da ake samun tashe-tashen hankula a fadar kasar nan.
Ya kuma bukaci manyan jami’n yan sanda na shiyyoyi da su gudanar da sinitiri a wuraran bauta, filan jirgen kasa,manyan hanyoyi, da wuraran ajiye mota, filin jirgin sama da hanyoyin ruwa bankuna da sauraran muhimman wurare.
Babban safeton yan sandan, ya ce ya kamata a dauki mataki domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar saboda samun kwanciyar hankali a kasa baki daya.
Kazalika, ya ba da umarnin ga duk jami’ai da aka tura domin gudanar da wadannan ayyuka da su bada cikakken kulawa da bin doka, da hukunta masu aikata laifuka tare da shirye-shiryen magance matsalar tsaro yayin bukukuwan Easter.

Leave a Reply

%d bloggers like this: