Rundunar Sojin Nigeria Tayo Nasarar Kashe Mayakan Boko Haram 48

0 76

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram 48, sannan wasu 974 sun ajiye makamai tare da miƙa wuya.
Daraktan yaɗa labaran hedkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana wa manema labarai cewa ƴan ta-da-ƙayar-bayan sun miƙa wuya ne haɗe da iyalansu cikin makonni biyu da suka gabata.
Ya ce rundunar ta yi amfani da salo iri daban-daban wajen kai hare-hare “a kan ƴan ta’addan Boko Haram”.
Danmadami ya ce dakarunsu na Operation Haɗin Kai sun ƙaddamar da wasu hare-hare a kan ƴan Boko Haram ranar 23 ga watan Maris, cikin ƙananan hukumomin Askira Uba da Mafa da kuma Bama, inda suka kashe bakwai daga cikinsu yayin da wasu kuma suka tsere.
Ya ce sun yi nasarar ƙwato kayayyaki da makamai masu yawa kama daga kayan haɗa bama-bamai da kekuna da babura da sauransu.
Danmadami ya ce sun kuma samu nasarar tarwatsa maɓoyar ƴan ta-da-ƙayar-bayan abin da ya yi sanadin mutuwar da dama a cikinsu da jikkata wasu.
Ya ce hare-haren da suka ƙaddamar da jiragen sama kuma, sun lalata kayayyakin ƴan Boko Haram.
A baya-bayan nan, dubban mayaƙan Boko Haram ne suka miƙa wuya ga sojojin Najeriya, mai yiwuwa saboda matsin lambar da suke fuskanta daga dakarun ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: