Har Yanzu Gwamnatin Nigeria Bata Biya Mana Bukatun Mu Ba – ASUU

0 89

Kungiyar Malaman Jami’o’I ta kasa ASUU tace kawo yanzu gwamnatin tarayya bata yi cikakken bayani ba dangane da wasu bukatun kungiyar da yasa tayi yajin aiki.
ASUU, a shekarar data gabata ta janye yajin aikin data shafe watanni 8 tana yi bayan tayi mabanbanta zaman da gwamnatin tarayya.
Kungiyar ba neman gwamnatin tarayya ta bada kudin gyaran jamio’I, da cika alkawarin yarjejeniyar shekarar 2009 da kuma sakin kudin alawus-alawus ga malaman jami’o’I da sabon tsarin biyan malamai na UTAS.
Kungiyar tace haryanzu gwamnati bata yi wani bayani ba dangane da bukatun su.
Shugaban kungiyar Farfesa Emmaneul Osodeke ya kuma yi magana dangane da kudin da gwamnati ta fitar Naira Bilyan 320.3 domin jami’o’i.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa fitar da wadannan kudade,inda ya bukaci a kara kudin domin ya cika kashi 90 domin manyan makarantu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: