Yansanda sun Damke Wasu Masu Maganin Gargajiya da Sassan Jikin Mutane

0 168

A yaune Juma’a ne rundunar yansanda a garin Ibadan ta gurfanar da  wasu mutane 2 dake sana’ar maganin gargajiya gaban Kotun Majistire bayan kama su da laifin mallakar sassan jikin mutum.

Ana dai zargin Ifatunji Alade da Ifaniyi Alabi da laifin hadin baki gami da mallakar sassan jikin mutum, laifin da suka musanta aikatawa.

Dansanda mai gabatar da kara a gaban kotu Sajan Phillip Amusan, ya shaidawa kotun cewa an kama wadanda ake zargin ne ranar 21 ga watan Yuni da karfe 1:00pm na dare a kauyen Onipe, dake hanyar Ibadan /Ijebu – Ode kuma a lokacin a tare da su akwai wasu sassan jikin mutum.

Ya kara da cewa wannan abinda suka aikata laifi ne da ya sabawa sashi na 242 (1) (b) da sashi 517 na kundin sharia’ar manyan laifuka na jihar na shekara ta 2000.

Lauyan wadanda ake kara Bolarinwa Lawal, ya roki kutun da ta taimaka ta bayar da wadanda yake karewa beli a cikin sharuddai saukaka ba masu tsauri ba.

A don hakan ne alkaliyar dake sauraren shari’ar Mrs Odunola Latunji, ta bayar da belin wadanda ake karar kan kudi N200,000 tare da kawo mutane biyu kowannensu da yake da kimar irin wannan kudi.

Mai shari’ar kuma ce dole guda daga cikin wadanda zai tsaya musun ya kasance dan uwa ga wanda ake zargin yayinda dayan kuma zasu iya kawo kowanene amma wanda yake aikin gwamnati da yakai mataki na takwas.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa bayan sanya wadannan sharuddan bayar da belin masu maganin gargajiyar, alkaliyar ta dage sauraren karar har sai nan da ranar 8 ga watan Agusta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: