Da Alamun Samun Ambaliyar Ruwa – NEMA

0 171

Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta shawarci mutanen dake zaune a gabar kogunan Kwara da Binuwai a Jihohin Adamawa da Taraba da su sauya matsugunnai saboda gujewar ambaliyar ruwa.

Shugaban Aikace-Aikace na hukumar ta NEMA, Mista Abbani Garki ne ya bayar da wannan gargadin yayin rarraba kayayyakin taimako ga wadanda suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwan a Karamar Hukumar Yola ta Kudu ta Jihar Adamawa.

Garki yace hukumar ta karbi rahoton hasashen ruwan sama na shekarar da muke ciki ta 2019 daga hannun hukumar kula da yanayi ta kasa, wanda ya nuna cewa jihohin 30 ne ambaliyar ruwan sama zata shafa a bana.

A cewarsa, hukumar ta NEMA tare da takwarorinta na Jihohin na aiki tare tare da saka ido ko da za a nemi agajin gaggawa.

Yace akalla mutane 3,000 ne wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bara a Jihar Adamawa, Gwamnatin Tarayya ta taimakawa da kayayyakin masarufi dana rayuwa ta yau da gobe daga watan Janairu zuwa yanzu.

Garki yace kayayyakin taimakon da aka rarraba sun hada da kayan abinci dana gini da kayan masarufi, kekunan dinki da injinan nika da sauransu.

Daga karshe ya shawarci wadanda suka amfana da kayan da suyi amfani dasu kamar yadda ya kamata domin inganta rayuwarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: