‘Yan’uwan yaran da aka tsare kan zargin yin zanga-zanga sun nemi ayi musu adalci.

0 155

‘Yan’uwan yaran da aka tsare kan zargin yin zanga-zanga a Kano da Kaduna sun koka kan a yi masu adalci.

Iyaye da ƴan uwan yaran sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa yaran su basu da hannu kan zargin da ake masu na cin amanar ƙasa, inda suka roƙi hukumomi da su sakar masu ƴaƴansu.

Mutanen sun bayyyana cewa su talakawa ne basu da ƙarfin da za su cika dukkan sharuddan beli da kotu ta bayar a Abuja.

An kama masu zanga-zangar 76 a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa daga ɗaya zuwa 10 ga watan Agusta, inda aka gurfanar da su a gaban babbar kotun Abuja a ranar Juma’a.

Al’umma a faɗin Najeriya na ci gaba da bayyana takaicinsu kan bidiyon yaran da aka gurfanar gaban kotu daga wasu jihohin arewacin ƙasar.

Yaran waɗanda gwamnati ta zarga da cin amanar ƙasa, sun bayyana a hotuna da bidiyo mabanbanta cikin yanayi na galabaita, ta yadda wasunsu ko tsayuwa ba sa iya yi. Masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi Allahwadai da wannan mataki na kai yara ƙanana gaban kotu, tare da bayyana shi a matsayin cin zarafinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: