Yara 55,774 Aka Yiwa Allurarar Riga Kafin Cutar Polio A Jigawa

0 213

Hukumar kiwon lafiya ta jihar jigawa (JPHCDA) tace ta yiwa kananan yara 55,774 allurara riga kafin kamuwa da cutar Shan inna a karamar hukumar Mallammadori a watan Afrilu.

Babban jami’in shirye-shiryen hukumar a jihar Alhaji Usman Bilyaminu, ya sanar dahaka a Mallammadori.

Yace anyi anfani da allurer riga kafin cutar shan inna dubu 59,300 da aka digawa kananan yara a fadin jihar da kasha bakwai daga cikin dari.

Bilyaminu ya godewa karamar hukumar da ta bada gudummowar Biskit da Cakuleti ga kananan yara a lokacin da kayi digon maganin.

Yace kimanin maaikata, 109 aka dauka domin gudanar da aikin allurer riga kafin Polio din da aka fara a ranar Talata.

Yayi kira ga Iyaye da sarakunan gargajiya da su bada hadin kai tare da ilmantar da al’umar syu muhimmancin wannan Allurar riga kafin cutar.

Madogara – VON

Leave a Reply

%d bloggers like this: