Abinda Fadar Shugaban Kasa Ta Fada Kan Yadda Majalisa Ta Tantance Ministoci

0 133

Fadar Shugaban Kasa ta yabawa Majalisar Dattawa bisa tabbatar da mutanen da za a nada ministoci, bayan tantance su cikin gaggawa.

Babban Mataimakin Shugaban Kasa kan Kafafen Yada Labarai, Mallam Garba Shehu, shine yayi wannan yabon cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

Cikin mataimakin shugaban kasar, tsaurara bincike yana nufin shugabanci na kwarai ba wai cushewar aiki ba.

Daga nan sai yayi kyakyawan zaton majalisar ta 9 tare da majalisar zartarwa, zasu shayar da yan Najeriya romon demokradiyya cikin kankanin lokaci.

Majalisar ta Dattawa ranar Talata ta tabbatar da mutane 43 da za nada ministocin gwamnatin tarayya.

Ranar 23 ga watan da muke ciki na Yuli, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saki sunayen mutanen 43, ya aika dasu Majalisar Dattawa domin tantancewar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: