Yara 600,000 Ne Ba A Yi Musu Rigakafin Cututtuka Ba A Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa – UNICEF

0 59

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce sama da yara dubu 600 ne ba a yi musu rigakafin cututtuka masu kashe kananan yara a jihohin Kano, Katsina da Jigawa ba.

Shugabar ofishin UNICEF ta Kano, Rahama Farah ce ta sanar da hakan a yayin wani taron karawa juna sani game da Hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya ta 2023 a jiya.

Wani kwararre a fannin sadarwa na UNICEF, Samuel Kaalu ya yi kira ga masu kula da su, da su rungumi rigakafi domin rage mutuwar yara kananan a jihohin.

Da take magana kan yanayin Kawar da cuttuttukan dake addabar kanana yara a ofishin hukumar dake Kano, Rahama ta ce Kano ce ta fi kowacce yawan yara sama da dubu 300 daga cikin adadin wanda ya nuna tanada kashi 55 cikin 100.

Rahama Farah ta kara da cewa wannan matsalar ta shafi Yaran dake kananan hukumomi 46, kuma akasarin wadanda abin ya shafa a Kano suke zaune.

Leave a Reply

%d bloggers like this: