Da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, an yi bikin ban kwana da masanin kimiyya na kasar Sin marigayi Yuan Longping, wanda ya yi fice saboda kirkiro fasahar tagwaita irin shinkafa, a gidan jana’izar tsaunin Mingyang dake birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin.

Al’ummomin wurin sun yi tattaki zuwa tsaunin Mingyang domin ban kwana da Yuan Longping. Jama’a sun rika nuna girmamawa da ajiye furanni a gaban hotonsa. Wasu dake nesa da wurin sun yi ban kwana da marigayi Yuan ta wasu hanyoyi na daban.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: