Za a bawa Najeriya tallafin kudi Euro miliyan 25 don aikin samar da wutar lantarki a kasar

0 99

Gwamnatin tarayya da hukumar raya kasashe ta kasar Faransa a jiya sun rattaba hannu kan tallafin kudi na Euro miliyan 25 don aikin samar da wutar lantarki a kasarnan.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, kungiyar Tarayyar Turai da Hukumar Raya Kasashe ta Faransa ne ke daukar nauyin shirin na samar da wutar lantarkin, yayin da Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na kasa TCN ke aiwatar da shi.

Da yake jawabi a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar a Abuja, karamin ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Clement Agba ya ce, aikin ya yi daidai da manufofin shirin raya kasa na shekarar 2021 zuwa 2025.

Clement Agba ya ce sanya hannu kan yarjejeniyar ya nuna cewa Najeriya na kan hanyar aiwatar da shirin raya kasa.

A nasa bangaren, Manajan Daraktan Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na kasa, Sule Abdulaziz, ya mika godiyarsa ga gwamnatin Faransa da Tarayyar Turai bisa goyon bayan da suke baiwa Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: