Za’a yi zaman makoki na kwanaki uku a kasar Kenya biyo bayan mutuwar dalibai 17

0 97

An ayyana zaman makoki na kwanaki uku a Kenya, bayan mutuwar dalibai 17 a wata mummunar gobara a makaranta.

Shugaban ƙasar, William Ruto, ya ce za a gudanar da binciken kan yadda wannan lamari ya auku, kuma duk waɗanda aka samu da laifin sakacin aukuwar gobarar za su fuskanci hukunci.

Iyaye da dama na cikin zullumi da fargabar ko ɗaliban da ake cewa ba a gani ba akwai ‘ya’yansu a ciki.

Dalibai 17 suka kone kurmus – ta yadda ma ba za a iya gane su ba – a gobarar da ta tashi a jiya Juma’a a makarantar da ke tsakiyar gundumar Nyeri a birnin  kasar Nairobi.

Sama da mutane 2,000 ne suka yi kokarin ceto yaran, waɗanda galibinsu suka shige karkashin gadajen kwanansu a lokacin gobarar.

‘Yan sanda sun ce sai an yi amfani da gwajin ƙwayoyin halitta na DNA wajen tantace gawarwakin waɗanda suka mutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: