Hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa tare da babban bankin kasa CBN sun kaddamar da wani shirin bayar da horon sana’o’i ga yan gudun hijira dubu 350 wadanda rikici ya raba da muhallansu a yankin arewa maso gabas.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar a Maiduguri, kwamishinan tarayya na hukumar, Bashir Muhammad, yace shirin wani bangare ne na kokarin hukumar wajen dawo da rayuwa kamar yadda aka saba ga yan gudun hijira a Najeriya.

Yace duk wanda zai ci gajiyar shirin, yana da damar zaben koyon sana’o’i sama da kala 50, da suka hada da aikin hannu da kasuwanci da noma da sauransu.

Bashir Muhammad yace wadanda suka shiga shirin za kuma a basu horo tare da jari domin dogaro da kawunansu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: