Ƴan sanda sun karɓi cin hancin naira biliyan 44 a cikin watanni 3 da sanya dokar hana fita – Rahoto

0 327

Dai dai lokacin da ake cika watanni 6 da bullar cutar coronavirus ko kuma COVID-19 a duniya, wata kungiyar fafutuka mai suna International Society for Civil Liberties and Rule of Law (Intersociety), ta yi zargin cewa jami’an tsaron Najeriya da shugabanninsu sun samu makudan kudi lokacin dokar kulle.

Tun da farko gwamnatin tarayya da wasu gwamnonin jihohin ƙasar nan ne suka kafa dokar hana fita da sufuri domin takaita yaduwar cutar Korona.

Binciken kungiyar Intersociety ya nuna cewa cikin watanni 3, tsakanin 30 ga Maris zuwa 30 ga Yuni, jami’an tsaro sun karbi akalla naira biliyan 44 a matsayin cin hanci da toshiyar baki a wajen mutane.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya a birnin Onitsha da ke jihar Enugu, mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Emeka Umeagbalasi, sanarwar ta ce bincikensu ya kasance ne kadai kan masu motoci a cikin gari da iyakokin ƙasar nan amma banda jiragen sama da na ruwa.
Ƙungiyar ta ce jami’an tsaron da su ka karɓi waɗannan makudan kudaden na cin hanci sun hada da Sojoji, ƴan sanda, jami’an kiyaye afkuwar hadura akan titi, jami’an NSCDC (Sibil defense) da jami’an kwastam.

Hakazalika an samu jami’an Sojin sama da na ruwa da kashi a gindi, musamman lokutan da aka sanya su kan titi ko cikin rundunar kare iyakokin ƙasar nan domin hana mutane shigowa cikin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: