Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 kuma sun babbake gidaje 250 a jihar Filato

0 189

Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 kuma sun babbake gidaje 250 a masarautar Miango dake karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Ƴan bindigan sun kai wa masarautar hari ne a daren Asabar.

Sakataren yaɗa labaran kungiyar Iregwe Davidson Malison ya sanar da haka ranar Lahadi a garin Jos.

Malison ya ce maharan sun lalata gonaki sama da 40 a masarautar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: