Sabbin Shugabannin Ƙananan hukumomi 27 na Jihar Jigawa Sun San Matsayinsu

0 104

sababbin zababbun shugabannin kananan hukumomi 27 na Jihar Jigawa sun karbi takardun shaidar samun nasara zabensu daga hukumar zabe mai zaman kanta ta Jahar Jigawa.

Shugaban Hukumar Alhaji Ahmad Sani ne ya mika takardun ga zababbun shugabannin kananan hukumomin a wani taro da aka shirya a Dutse.

Ahmad Sani ya shawarci shugabannin da su jawo jama’a a jiki ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.

Shubagan Hukumar Zaben ya mika sakon godiya ga jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro da kuma kungiyoyin tallafi na kasa da kasa musamman wata gidauniyar tallafawa harkokin zabe ta kasa da kasa mai suna ‘International Foundation for the Electoral System’ wacce ta bayar da gagarumar gudunmawa dan ganin samun nasarar zaben.

Ahmad Sani ya kara da cewa Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta ta Jihar ta samar da alakar aiki ta kut da kut tsakaninta da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa wato INEC a bangaren horon ma’aikata wanda ya taimakawa hukumar matuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: