Shugaba Buhari Ya Bayyana Wadanda Zasu Taimaka Masa A Mulkinsa

0 101

Shugaba Buhari yace yana bukatar ingattacciyar majalisar zartarwa da zata taimaka masa wajen cika alkawarukan daya dauka ga ‘Yan Najeriya.

Shugaban ya fadi hakanne a lokacin daya karbi bakuncin yan kungiyar yada labaru na Buhari wato ‘Buhari Media Organization’ a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Buhari yace zai yi aiki tukuru dan ganin yabar kasar ta samu cigaba fiye da yadda ya sameta.

Ya bayyana kungiyar ta ‘Buhari Media Organization’ a matsayin wani ginshiki a bangaren yada labarai na gwamnatinsa, ya kuma jinjinawa yan kungiyar akan rawar da suke takawa.

Kazalika Buhari ya nanata kokarinsa na ganin bayan tabarbarewar rashin tsaro inda ya bayyana cewa burinsa yaga Najeriya ta zama kasa mai zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.

Tunda farko, shugaban kungiyar, Omoniyi Akinsiju ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari tayi kokari matuka fiye da gwamnatocin da suka gabata

Manema labaru sun rawaito cewa wani dan jarida da Buhari ya garkame a zaman mulkinsa na soja mai suna Tunde Thompson na daga cikin yan kungiyar ta BMO.

Leave a Reply

%d bloggers like this: