Majalisar Dattijai Zata Nemo Mafita Ga Matsalar Karancin Zuwan Yara Makaranta

0 81

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya nuna damuwa dangane da karuwar yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya wadanda yace sun kai kimanin miliyan 10.

Ahmad Lawan ya fadi hakanne yayin da yake maraba da sanatoci 109 na sabuwar majalisa a zauren majalisar dattawa.

Yace matsalar yaran dake barin makaranta tana bukatar kulawa ta musamman a wajensa, a matsayinsa na tsohon malamin jami’a, sannan kuma wannan sabuwar majalisar ta 9 zatayi kokarin ganin an shawo kan matsalar.

Lawan yace matsalar rashin daidaito da kalubalen rashin tsaro sune manyan kudirorin da za asa a gaba a wannan majalisar.

Manema labaru sun rawaito cewa majalisar ta dattawa ta kaddamar da wani kwarya-kwaryan kwamiti mai mutane 13 bisa jagorancin sanata mai wakiltar kebbi ta tsakiya Alhaji Adamu Alero, dan tsaro tare da shiryo kudirorin da majalisar zata saka a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: