Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana cewa za’a fara gudanar da Rijistar masu kada kuri’u a ranar 26 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki.

Tunda farko hukumar ta sanar da ranar 19 ga watan da muke ciki a matsayin ranar fara gudanar da Rijistar, sai dai hukumar ta dage hakan daga baya, saboda hukun Sallah da gwamnatin tarayya ta bayar.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Fadakar da Al’umma kan Zabuka na hukumar INEC Mista Festus Okoye, ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa hakan ya zama dole biyo bayan hutun Sallah da gwamnatin tarayya ta bayar a ranakun 20 da 21 ga watan Yuli.

A ranar 28 ga watan Yuni ne hukumar INEC ta kaddamar da Shafin Yanar Gizo, ta yadda Masu kada’uri zasu iya yin Rijista ta shafin yanar gizo, inda kuma zasuje ofishin hukumar na kananan hukumomin domin kammala sauran Rijistar ta zahiri.

Hukumar ta ce kashi 66 cikin 100 na Mutanen da sukeyi Rijistar ta shafin yanar gizo Matasa ne.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: