Yadda aka damke wani Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na bogi a Kano

0 78

Runduanar yan sandan jihar kano ta kama wani Muhammad Aliyu da ya ke yin karya cewa shi maataimakin kwamishin yan sanda ne kuma kwamandan rudunar kwantar da tarzoma, rundana ta 52 da ke amfani da sunan domin damfarar mutane.

Rundunar ta bakin kakakinta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa tace biyo bayan umarnin kwamshinan yan sandan jihar CP Isma`ila Shu`aibu Dukko, sun yi nasarar cafke Muhammada Aliyu “wannan mutum da kuke gani da takardu a hannunsa da kuma wani complimentary cerd da alluarai yana zuwa gurare da dama yana nunawa mutane cewa shi fa dan sanda ne babba, mataimakin kwamshinan yan sanda wato shi kwamanda ne ma wanda yake kula da yan sandan kwantar da tarzoma na 52 duk inda yaje yana nunawa mutane shi mataimakin kwamishinan yan sanda ne kuma ya cuci mutane da dama.

“Haka zalika lokacin muka kama shi mun kama shi da wannan kati da yake nunawa da kuma wadannan takardu da kuke gani wanda yaea nuna cewa fa shi likita ne wanda an gurfanar da shi a gaban kotu a baya na wannan abunda yake, bincike da muka gudanar mun gano cewa wannan ba likita bane dama ba dan sanda bane ya zalinci mutane da dama”, inji Kiyawa.

Cikin wani faifan bidiyo da Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda ake zargin Muhammad Aliyu mazaunin unguwar Hotoro da ke birnin Kano me shekaru 45 ya ce, duka takardun da aka samu a hannunsa nasane kuma sunansa ne a jike “ni ba dan sanda bane nayi kuskure bazan karaba”.

Daga karshe Kiyawa ya ce “daga kama shi mun samu masu korafi a kansa daga mutane 4 wadanda mutum biyu a ciki ya karbar musu kudi, wasu kuma ya duba su a matsayin basu da lafiya, kwamishinan yan sanda na jihar Kano CP Isma`ila Shu`aibu Dukko, ya ba da umarni a maida shi babban sashen binciken manyan lefuka dake Bamfai wanda za a fadada bincike, da zarar an kammala bincike ko shakka babu za a mika shi gaban kotu”.

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Leave a Reply

%d bloggers like this: