Ba za a yi bukukuwan Babbar Salla ba, inji gwamnatin jihar Jigawa

0 80

Har yanzu dai ana ta musayar yauwa gameda da zartarwa da gwamnatin jihar Jigawa tayi na dakatar da bukukuwan babbar salla a dukkannin masarautun jihar nan guda biyar sakamakon shawarwarin kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar corona na kasa.

Tun jiya ne wata sanarwa ta fita wacce take kunshe da dalilan da yasa aka dakatar da bukukuwan inda da sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, yace an bada umarnin gudanar da sallar Idi a filayen Idi da kuma masalatan Juma’a tare da takaita yawan taruwar jama-a domin gudun samun cinkoso.

Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini yace dakatarwar ta biyo bayan shawarwarin da kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar corona ya baiwa jihohi na yin amfani da dokokin kariya daga kamuwa daga cutar corona sakamakon bullar nauin cutar corona mai lakanin Delta variant of COVID-19.

Sanarwar ta taya alummar musulmi murnar bukukuwan babbar salla tare da yin kira ga shugabannin addinai dasu kiyaye domin gudun kamuwa daga cutar a cikin alumma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: