Shugaba Buhari ya amince da bada Naira Biliyan 6.25 ga Jihar Katsina domin shirin killace dabbobin Fulani a jihar

0 78

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da bada Naira Biliyan 6.25 ga gwamnatin Jihar Katsina domin fara aiwatar da shirin Killace Dabobin Fulani a jihar.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, ya rabawa manema labarai a Abuja.

A cewar sanarwar, Gwamna Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa bada kudaden zai taimakawa shirin gwamnatin tarayya na killace dabobin Fulani a wuri guda a kasa baki daya.

Da yake Jawabi a lokacin kaddamar da Madatsar Ruwa ta Zobe wanda aka kammala bayan watsi da ita tsawon kimanin shekaru 29, Gwamna Masari, ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa yadda yake samar da ayyukan cigaba, tare da fitar da Naira Biliyan 5 domin fara aikin.

Gwamna Aminu Bello Masari, ya ce kammala aikin tashar Madatsar ruwa ta Zobe, wanda gwamnatin tarayya ta kammala, zai samarda Ruwan sha Lita Miliyan 50 ga mutanen da suke karkara.

Kazalika, ya godewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bisa kaddamar da aikin, tare da Kaddamar da Aikin Hanyar Dutsinma-zuwa Tsaskiya mai nisan Kilomita 50.

Leave a Reply

%d bloggers like this: