Hukumar Shige da Fice ta Kasa wato Immigration reshen jihar Jigawa, ta kubutar da Mata 4 daga hannun masu safarar mutane a jihar nan.

Kwanfuturolan Hukumar na Jihar Jigawa Malam Isma’ila Abba, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, inda ya kara da cewa an kubutar ta mutanen ne a kyauyen Gurai na karamar hukumar Babura.

A cewarsa, Jami’ansu ne wanda suke aiki a Mahadar Kazaure-Babura-Ringim ne suka kubutar da Matasan.

Haka kuma ya ce shekarun Matasan da aka kubutar din bai wuce 16 zuwa 33 ba, kuma suna kokarin tsallaka iyakar Jigawa da Katsina domin zuwa Birnin Tripoli na kasar Libya.

Kwamandan hukumar ya ce Matasan sun fito ne daga Jihohin Akwa Ibom da Lagos da Ogun da kuma Osun.

Kazalika, ya ce zasu mika Matasan ga hukumar Yaki da Safarar Mutane domin cigaba da bincike.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa a watan Mayun daga gabata, kimanin Mata 7 hukumar ta kubutar daga hannun masu safarar mutane wanda suke kokarin tsallakawa dasu zuwa Libya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: