Sarkin Gumel ya karrama Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya dake Dutse da Alkalin alkalan jihar Jigawa.

Mai martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani II (CON) ya karrama Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed da Alkalin alkalai na jihar Jigawa, mai shari’a Umar Sadik kan nadin da aka yi musu kwanan nan.

Sarkin wanda ya nuna godiyarsa ga Allah kan wannan nadi da aka yi musu, ya roki Allah Ya ba su karfi da hikima don sauke nauyin da aka dora musu yadda ya kamata.Sarkin wanda daga baya ya gabatar da wasikar girmamawa ga wayanda aka nada, ya ce masarautar Gumel tana alfahari da nasarorin da suka samu.

Sarkin ya yi addu’ar zaman su ya kawo daukaka ga jihar ta Jigawa da ma Najeriya baki daya.

A jawabin Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya gode wa mai martaba sarki da mambobin majalisar masarautar bisa karrama su da akayi. Ya kuma kara da cewa zai ci gaba da yin bakin kokarinsa don kawo wa cigaba ga jami’ar, Jigawa dama Najeriya baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: