A ranar Alhamis, shugabannin kasashen Afirka 11 suka bukaci samun rancen makudan kudade da suka ce za su yi amfani da su wajen zaburar da tattalin arzikinsu da corona ta shafa.

Shugabannin na Afirka sun gana ne a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast, inda suka yanke shawarar neman dala biliyan 100 daga wani bangare na bankin duniya da ke bayar da lamuni ga kasashe masu raunin arziki.

Galibin kasashen Afirka dai ba su fuskanci ta’adin corona ta fuskar kamuwa da kuma mace-mace kamar yadda aka gani sauran sassa na duniya ba.

Sai dai matakan kulle da kuma na hana tafiye-tafiye, sun jefa kasashen na kudu da hamadar Sahara cikin yanayi na tawayar tattalin arziki.

Mutum miliyan 18 ne dai aka yi wa rigakafin corona a Afirka mai yawan al’uma biliyan daya da dubu 300, abin da ke kara fargabar tsawaita halin da suke cikin, yayin da su kuwa manyan kasashen ke sake bude harkokinsu bayan matsin da suka sha daga corona.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: