Gwamnatin jihar jigawa ta dauki matakan farfado da fannin ilimi

0 59

Gwamnatin jihar jigawa ta dauki matakan farfado da fannin ilimi domin bunkasa hazakar daliban dake makarantun gwamnati.

Mataimakin Gwamnan jiha Malam Umar Namadi ne ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga hukumar bada ilimi bai daya ta kasa a ofishin sa.

Yace jihar jigawa na sahun gaba a ayyukan hukumar wanda hakan ya taimaka wajen inganta yanayin koyo da koyarwa a jihar nan.

Umar Namadi ya kara da cewa bayan haka gwamnati ta dauki sabbin malaman makaranta da basu horo da kuma sake horas dasu domin dalibai su sami ilimi mai inganci.

Tun farko a nasa jawabin Jagoran Tawagar, Dakta Tom Onyekere ya ce sun ziyarci jihar jigawa ne domin duba ayyukan da hukumar ilimi a matakin farko ta jiha da tarayya suka gudanar a jihohin da jam’iyyar APC ke milki.

Dakta Tom ya kara da cewa a lokacin ziyarar zasu duba kayan koyarwa na zamani da yin amfani da manhajar koyarwa data dace inda a karshe zasu fidda matsayin kowace jiha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: