A ƙalla mutum 30 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wani bam ya tashi a wani masallacin mabiya Shia yayin da ake gabatar da Sallar Juma’a a birnin Kandahar na Afghanistan.

Hotunan cikin masallacin na Iman Bargah sun nuna yadda tagogi suka farfashe sannan ga gawarwaki a zube birjik.

Har yanzu ba a gano abin da ya jawo tashin bam din ba, amma ana tsammanin aikin ƙunar baƙin wake ne.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya ji ƙarar fashewa har sau uku.

Wannan na zuwa adaidai lokacin da Dakarun Taliban na musamman suka killace wajen suka kuma umarci mutane da su ba da taimakon jini ga marassa lafiyan.

A cewar wani wakilin BBC Secunder Kermani ya ce wani sashe na ƙungiyar IS ce ake zaton ta kai harin.

Taliban ta ƙwace iko da Afghanistan bayan da dakarun ƙasashen sun janye daga ƙasar a ƙarshen watan Agusta bayan yarjejeniyar da aka cimma da Amurkan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: