Abin Alheri ya Sami Mayankar Dabbobi Ta Auyo a Jigawa

0 88

Kungiyar masu sana’ar fawa ta kasa reshen jihar Jigawa, ta yabawa karamar hukumar Auyo bisa daga darajar gidan mayankar dabbobi ta karamar hukumar.

Alhaji Adamu Dan- Sifiringa mai Magana da yawun kungiyar ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Auyo. Yace mayankar ta garin Auyo ta lalace ne tun kafin ruwan sama ya kara lalata a shekarar 2018.

Dan-Sifiringa ya kara da cewa mayankar yanzu ta kasance ta zamani inda take dauke da kayayyaki masu inganci da nagarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: