Abin Tashin Hankali Ne Ace Har Yanzu Akwai Sauran Yan Matan Chibok A Hannun ‘Yan Boko Haram

0 72

Asasun kula da yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cewa abu ne mai tashin hankali kasancewar har yanzu akwai sauran yanmatan Chibok da ‘yan Boko Haram suka sace daga makaranta a jihar Borno wadanda ke tsare tsawon shekaru tara.
An sace yanmatan Chibok a daren ranar 14 ga watan Afrilun 2014, lamarin da ya jawo Allah wa dai a kasashen duniya.
Asusun na majalisar dinkin duniya, cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, yace har yanzu rikici a bangaren kasarnan na cigaba da shafar yara mata da maza.
A wani batun kuma, asusun na UNICEF ya kara da cewa karin dubban yara mata da maza na cigaba da fuskantar cin zarafi a rikicin dake cigaba da aukuwa a yankin, lamarin dake nuna bukatar kare yara a kasarnan.
Asusun na majalisar dinkin duniya ya fada a ranar 7 ga watan Afrilu cewa ‘yan bindiga sun sace wasu yara 80 a yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Cristian Munduate, tace ana cigaba da fuskantar tashin hankali a yau kasancewar har yanzu ana sace yara da kashe su ko raunata su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: