‘Abu ne mai wahala mu iya zuwa makarantun da muke koyarwa saboda rashin kudaden da muke fuskanta a yanzu’ – Shugaban ASUU

0 78

Shugaban kungiyyar malaman jami’oi ta kasa ASUU Prof Emmanuel Osodeke yace abu ne mai wahala membobin kungiyyar su iya, zuwa makarantun da suke koyarwa saboda rashin kudaden da suke fuskantar a halin yanzu.

Prof Emmanuel Osodeke ya bayyana hakan ne a jiya da yamma a lokacin dayake zantawa da gidan Telebijin na Channels cikin wani shiri mai suna Politics Today.

Ya kara da cewa mafi akasarin malaman da suke koyarwa, ba’a cikin jami’oin suke zaune da iyalansu ba, saboda rashin wadataccen gidaje.

Prof Emmanuel Osodeke ya kara da cewa shafe watanni 8 suna gudanar da yajin aiki ya jefa Malaman cikin tsananin talauci, saboda abu ne mai wahala mutum ya iya shafe watanni 8 babu Albashi.

Tare da jaddada cewa, mafi akasarin malaman yanzu haka basu da kudin zirga-zirga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: