Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya kone kayayyakin da aka yiwa algus na kimanin naira miliyan biyu a Hadejia

0 78

Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa, ya kone kayayyakin da aka yiwa algus na kimanin naira miliyan daya da dubu 700 a kotun majistare ta Hadejia.

Shugaban kwamitin, Mallam Farouk Abdallah Mallam Madori ya sanar da hakan a lokacin bikin kone kayayyakin da aka yiwa algus a masarautar Hadejia.

Yace kayayyakin da aka kone sun hadar da takin zamani bahu 530, da bahunan shinkafa 14, da bahunan alkama 4, da bahunan ridi 4, da dusar Dangote bahu 16, da maganin kwari katan 7, da manja jarka daya, da waken suya bahu daya, da kuma sobo bahu daya.

Mallam Farouk Abdallah yana mai cewar an yi gwanjon kayayyaki na naira dubu 200 da aka yi yunkurin yi musu algus.

Yace kwamitin zai cigaba da kwace duk wani kayan da aka yiwa algus, inda ya nemi hadin kan jama’a a kowane lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: