An fara rabon tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa a jihar Jigawa

0 89

Kwamitin kiyasin hasarar da aka yi sanadiyyar ambaliyar ruwa, da tara gudunmawa da kuma raba tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa a jihar Jigawa ya fara zamansa na farko a birnin jiha, Dutse.

A jawabinsa wajen zaman kwamitin, shugaban kwamitin, Alhaji Bashir Dalhatu, Wazirin Dutse, yace aikin kwamitin ya hada da tantancewa da shiryawa da nemo gudunmawa da kuma raba tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa a jihar Jigawa.

Yace an kafa kwamitin ne a daidai lokacin da ya dace, kuma hakan zai bada dama ga gwamnati ta kara shiri domin tinkarar damina mai zuwa.

Bashir Dalhatu ya yi kira ga wakilan kwamitin su jajirce tare da bada tasu gudunmawa domin kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa.

Wazirin na Dutse ya kara da cewa kwamitin ya yanke shawarar ziyartar wuraren da ambaliyar ta yi ta’adi domin tantancewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: