‘Akwai dalilan da yasa aka wanke Nmandi Kanu’ -Kotu

0 78

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sallami shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu tare da wanke shi.

Shugaban kungiyar ta IPOB dai ya kasance yana fuskantar shari’ar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 15 da suka hada da cin amanar kasa da ta’addanci.

Da suke yanke hukunci a jiya a Abuja, alkalan kotun daukaka kara su uku karkashin jagorancin mai shari’a Jummai Sankey sun wanke Nmandi Kanu daga tuhumar da ake masa.

A halin da ake ciki, babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya ce shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu, har yanzu yana da tuhumar da zai amsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Umar Gwandu, ya fitar, ta ce kotun daukaka kara ta sallami Nmandi Kanu ne kawai a kan karar da aka shigar, ban da wasu batutuwan da suka shafi sauran laifukan da ya aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: