Wasu mutane uku da ake zargin masu fasa kwauri ne sun mutu a wani hatsarin mota a karamar hukumar Babura da ke nan jihar Jigawa

0 66

Wasu mutane uku da ake zargin masu fasa kwauri ne sun mutu a wani hatsarin mota a karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sitayari ya kwacewa direban wata mota kirar Honda akan hanyar Babura zuwa SuleTankarkar.

Ya ce a lokacin da motar ta isa kauyen Tsalle da ke da nisan kilomita uku daga garin Sule Tankarkar, direban ya rasa yadda zai yi ya sarrafa motar, sakamakon gudun wuce gona da iri.

Kakakin hukumar tsaro ta civil defense, Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce sitayari ya kwacewa direban motar inda ya bugi wata bishiya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutanen.

Adamu Shehu ya ce likitocin ne suka tabbatar da mutuwar wadanda suka mutu a karamin asibitin Sule Tankarkar.

Motar na dankare da kayan abinci da suka hada da buhunan fulawa da katan-katan na taliya da ake zargin an shigo da su ta barauniyar hanya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: