Shugaban karamar hukumar Kirikasamma ya umarci ma’aikatan kiwon lafiya da su sa ido akan ingancin abincin da ake bawa yara ‘yan makarantun firamare

0 64

Shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Isa Adamu Matara, ya umarci ma’aikatan kiwon lafiya da su sa ido akan ingancin abincin da ake bawa yara ‘yan makarantun firamare.

Ya bada wannan umarnin ne lokacin taro da jami’an kula da riga kafin cutar kyanda da korona a ofishinsa.

Shugaban karamar hukumar ya yabawa jami’an kiwon lafiya bisa kokarinsu na kai karamar hukumar ga mataki na uku wajen yaki da cutar korona a fadin jihar nan.

Isa Adamu Matara yace majalisar karamar hukumar za ta ci gaba da baiwa bangaren kiwon lafiya kulawar da ta dace domin inganta harkokin kula da lafiyar al’ummar yankin.

A nasa jawabin, shugaban hukumar hukumar lafiya matakin farko na karamar hukumar, Alhaji Musa Abdullahi, yace an yiwa mutane fiye da dubu 500 da 600 alluran riga kafi a mazabu goma na karamar hukumar a watan da ya gabata.

Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da su wayar da kan mutane akan gangamin rigakafin da za a fara a ranar 20 ga wannan watan da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: