Anyi zanga-zanga kan yadda wasu ‘yan China ke yankawa da kwashe jakuna ba bisa ka’ida ba a Abuja

0 96

Daruruwan masu zanga-zanga a jiya suka gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja, kan yadda wasu ‘yan kasashen waje musamman ‘yan kasar China ke yankawa da kwashe jakuna ba bisa ka’ida ba.

Zanga-zangar wacce ta gudana a dandalin Unity Fountain na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin kafa wata doka a majalisar dattawa domin daidaita kasuwancin jakuna a Najeriya.

Masu ruwa da tsaki da suka hada da ‘yan majalisa, da dillalan jakuna, da hukumomin gwamnati sun samu rarrabuwar kawuna kan kudurin dokar a yayin zaman majalisar ta dattawa.

Yayin da wasu ke ba da shawarar hana yanka jakuna saboda fargabar karewarsu, wasu kuma sun ce tsarin kasuwancin jakunan shi ne na dakile fasa kwaurinsu da kiwonsu wanda hakan zai magance karancinsu.

Masu zanga-zangar dai sun ce ana ci gaba da yanka jakuna babu kakkautawa duk da umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na dakatar da wannan matsala.

Leave a Reply

%d bloggers like this: